Bisa labarin da gidan talibijin na Al-Jazeera na kasar Qatar ya bayar a ran 17 ga wata, an ce, a birnin Ajdabiya, wato wuri mai arzikin man fetur dake gabashin kasar Libya, dakarun Gaddafi sun kai sabon hari kan dakarun adawa. Kakakin dakarun adawa ya ce, a ran 17 ga wata da safe, dakarun Gaddafi sun yi amfani da manyan bindigogin igwa wajen kai farmaki sosai kan kofar dake yammacin birnin, inda a kalla mutane 47 suka ji raunuka. Amma daga baya, dakarun adawa sun kori dakarun Gaddafi, kuma sun sake mamaye wannan kofa.
Bugu da kari, jiya, dakarun Gaddafi sun yi ta harba harsassan igwa kan birnin Misrata, lamarin da ya haddasa mutuwar mutane 6. Birnin Misrata shi kadai ke cikin hannun dakarun adawa yanzu, kuma dakarun Gaddafi sun riga sun kewaye birnin yau da tsawon wasu 'yan makonni. Bisa labarin da kafofin watsa labaru na kasashen yammacin duniya suka bayar, an ce, daruruwan fararen hula sun mutu sakamakon yakin a birnin Misrata. Sakamakon haka, babban kwamanda Abdul Fatah Younis na dakarun adawa ya bukaci kungiyar NATO da ta dauki kwararan matakan soja a kasar Libya. Ya bayyana cewa, idan dakarun adawa sun samu jiragen sama na soja masu saukar ungulu, tabbas ne za su iya kutsa layin dakarun Gaddafi wadanda suke kewayen birnin Misrata cikin sauki.