Haka kuma, hukumar sa ido kan hakkin bil Adam ta kasa da kasa da dakarun adawa na Libya sun zargi dakarun gwamnatin Gaddafi a ran 15 ga wata cewar dakarun Gaddafi sun yi amfani da bamabamai masu kwanso a kalla sau uku a unguwannin dake birnin, amma kakakin gwamnatin Libya Saleh Ibrahim ya musunta wannan zargi har sau da yawa a ran 16 da ran 17 ga wata. Malam Ibrahim ya ce, dakarun gwamnatin ba su da irin wadannan bamabamai masu kwanso.
Dadin dadawa, dakarun adawa ba su samu rinjaye ba a filin yaki. Ko da yake kungiyoyin adawa na Libya sun nemi kungiyar NATO da ta kara samar musu kudi da makamai, amma har yanzu ba a samu matsaya daya ba kan wadannan batutuwa a cikin kungiyar NATO. Sakamakon haka, ba a san yaya kungiyar NATO za ta iya kara tallafawa kungiyoyin adawa na Libya a nan gaba ba.