in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kasa samun sakamako a gun shawarwarin saukar da Gbagbo daga karagar mulkin kasar Cote d'lvoire
2011-04-07 13:44:28 cri

A hakika dai, an fara yin shawarwari ne bayan da Ouattara ya cimma nasarar yaki. Sojojin Ouattara sun kwace yankin kudancin kasar dake karkashin shugabancin Gbagbo a ran 28 ga watan da ya gabata, kana sun mamaye birnin Yamoussoukro dake tsakiyar yankin a ran 30 ga wata, sannan kuma, a ran 31 ga wata, sun kwace tasha mafi girma a duniya wadda kuma ta fitar da koko wato tashar San Perdro, daga bisani, a ran 4 ga wata, sun cimma nasarar daukar matakan soja a birnin Abidjan, kana sun kewaye fadar shugaban kasar.

Duk da cewar an kasa samu sakamako a gun wannan shawarwari, amma sojojin Ouattara sun cimma nasarar daukar matakan soja bisa goyon bayan MDD da kasar Faransa, a halin yanzu Laurent Gbagbo ba ya da wata mafita. Kana a ran 6 ga wata da safe, sojojin Ouattara sun yi yunkurin kai farmaki na karshe kan fadar Gbagbo.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China