in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kasa samun sakamako a gun shawarwarin saukar da Gbagbo daga karagar mulkin kasar Cote d'lvoire
2011-04-07 13:44:28 cri

Ministan harkokin waje na kasar Faransa Alain Juppe ya sanar a ran 6 ga wata cewa, an kasa samun sakamako a gun shawarwarin da MDD da kasar Faransa suka kira don kalubalantar Laurent Gbagbo da ya mika ikon mulkin kasar. Kafofin watsa labaru suna ganin cewa, ko da yake ba a samu sakamako ba a gun wannan shawarwari, amma bangarorin biyu dake kin jinin juna sun riga sun tsagaita bude wuta, idan za a cimma nasarar yin shawarwari a nan gaba, watakila za a iya kawo karshen yakin basasa na kasar Cote d'lvoire.

Mr. Juppe ya furta a ran 6 ga wata a majalisar dokoki cewa, wakilan bangaren Gbagbo da tsohon firaministan kasar Cote d'lvoire Alassane Ouattara sun yi shawarwari na wasu awoyi a ran 5 ga wata, amma ba tare da cimma wata nasara ba sabo da Gbagbo ya ki mika ikon mulkin kasar. Kafin haka, Mr. Juppe ya furta cewa, an riga an kawo karshen yake-yake a tsakanin bangarorin biyu, kuma za a yi shawarwari nan da nan domin tattauna yadda za a kalubalanci Gbagbo da ya mika ikon mulkin kasar da kuma amincewa da Ouattara a matsayin shugaban kasar.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China