in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun Laurent Gbagbo sun nemi a tsagaita bude wuta
2011-04-06 13:53:24 cri

Jiya 5 ga wata, babban hafsan hafsoshin rundunar tsaron kasar Kodivwa Philippe Mangou dake goyon bayan Laurent Gbagbo ya gaya wa manema labaru cewa, dakarun Laurent Gbagbo sun riga sun tsagaita bude wuta da dakarun dake goyon bayan Alassane Ouattara. Sabo da haka, ya nemi dakarun M.D.D. dake kasar Kodivwa su kuma tsagaita bude wuta. Sannan, a wannan rana, Mr. Alain Juppe, ministan harkokin wajen kasar Faransa ya ce, Laurent Gbagbo ya ba da sharadinsa na sauka daga mukamin shugabancin kasar Kodivwa.

Phillippe Mangou ya bayyana niyyar tsagaita bude wuta ne bayan da aka yi ta kai hare-hare kan birnin Abidjan, wato babban birnin kasar Kodivwa ta fuskar tattalin arziki cikin kwanakin da suka gabata. Birnin Abidjan ya kasance sansani na karshe ga Laurent Gbagbo, amma dakaru mabiyan Alassane Ouattara da na kungiyar M.D.D. da kasar Faransa sun yi hadin gwiwa sun kewaye shi a ran 4 ga wata. Hakan ya sa Laurent Gbagbo da mabiyansa sun shiga cikin mawuyacin hali.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China