in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An dauki matakan kawar da manyan makamai da sojojin Gbagbo suka mallaka
2011-04-05 17:57:09 cri

Ban Ki-Moon ya bayyana cewa, bisa kuduri mai lamba 1975 da kwamitin sulhun MDD ya zartas, ya bukaci kungiyar da MDD ta jibge a kasar Cote D'ivoire da ta dauki matakan soji da suka dace, a kokarin hana sojojin dake biyayya ga Gbagbo rika amfani da manyan makamai kan fararen-hula.

A wannan rana kuma, fadar shugaban kasar Faransa ta bayar da wata sanarwa, inda ta ce, sojojin kasar sun bada hannu ga matakan soja da kungiyar da MDD ta jibge a kasar Cote D'ivoire ta dauka, haka kuma ta ce, gwamnatin Faransa ta yi kira da a dakatar da duk wani matakin soja da ake dauka kan fararen-hula ba tare da bata lokaci ba, kuma za'a yanke hukunci mai tsanani kan wadanda suka aikata mummunan laifi.(Murtala)


1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China