in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An dauki matakan kawar da manyan makamai da sojojin Gbagbo suka mallaka
2011-04-05 17:57:09 cri

Bayan da aka gudanar da babban zabe a kasar Cote D'ivoire a watan Nuwamban shekarar da ta gabata, Laurent Gbagbo da tsohon firaministan kasar Alassane Ouattara sun sanar da kama aikin shugabancin kasar, lamarin da ya jefa kasar Cote D'ivoire cikin wani halin ja-in-ja, kuma an rika samun tashe-tashen hankali a kasar. Wasu kungiyoyin kasa da kasa, ciki har da Majalisar Dinkin Duniya, kungiyar tarayyar Afirka, da kungiyar tarayyar Turai sun amince da gwamnatin Ouattara, amma Laurent Gbagbo ya ki sauka daga karagar mulki. Sa'an nan kungiyar hadin-gwiwar tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS, da kungiyar tarayyar Afirka AU sun yi kokarin shiga-tsakanin rikicin siyasar kasar, amma kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba. Kwanan baya, sojojin dake biyayya ga Ouattara sun kai farmaki a muhimman birane biyu wato Abidjan da Yamousoukro, inda suka gwabza mummunan fada tare da sojojin Gbagbo, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar fararen-hula masu dimbin yawa.

Ranar 4 ga wata, kakakin sashin kula da harkokin kiyaye zaman lafiya na MDD ya fadi cewa, dakarun MDD dake kasar Cote D'ivoire sun fara daukar matakan soja a kan sojojin dake biyayya ga Laurent Gbagbo, a kokarin hana su amfani da wasu manyan makamai a kan fararen-hula da sojojin shimfida zaman lafiya. Wannan kakaki ya ce, a cikin 'yan kwanakin nan, sojojin Gbagbo suna kara amfani da manyan makamai kan fararen-hula da sojojin shimfida zaman lafiya dake wurin, shi ya sa kungiyar MDD ta dauki matakin soji bisa izinin kwamitin sulhu.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China