in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An dauki matakan kawar da manyan makamai da sojojin Gbagbo suka mallaka
2011-04-05 17:57:09 cri

A wannan rana kuma, sakatare-janar na MDD Ban Ki-Moon ya bayar da wata sanarwa, inda ya nuna damuwa sosai kan yanayin da ake ciki yanzu a kasar Cote D'ivoire, inda ya ce, a kwanakin baya, yanayin tsaron da ake ciki a kasar ya kara tabarbarewa, kuma rikici ya ci gaba da tsananta tsakanin sojojin dake biyayya ga Alassane Ouattara da na Laurent Gbagbo, lamarin da ya tsunduma kasar Cote D'ivoire cikin fadace-fadace, kuma fararen-hula da dama sun rasa rayukansu.

Mista Ban Ki-Moon ya ci gaba da cewa, a cikin 'yan kwanakin nan, sojojin dake biyayya ga Laurent Gbagbo sun kara amfani da wasu manyan makamai a kan fararen-hula dake Abidjan, har ma sun kai hare-hare kan hedkwatar kungiyar da MDD ta jibge a kasar, lamarin da ya raunata wasu ma'aikatan shimfida zaman lafiya hudu. Har wa yau kuma, wadannan dakaru sun kai farmaki a kan sojoji masu sintiri da MDD ta tura domin kiyaye fararen-hula da yin jigilar mutanen da suka ji rauni, har ma wasunsu sun ji rauni.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China