in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta cimma burin kafa tsarin dokokin gurguzu na musamman
2011-03-10 15:27:23 cri

Bisa kundin tsarin mulkin kasar Sin wato dokar kasar, an tsara dokokin tabbatar da kare hakkin jama'ar kasar. Alal misali, tabbatar da ikon dukiyar jama'a ya sa kaimi ga tsara dokoki kan wannan fanni, kana ya taimaka wajen kafa tsarin tattalin arziki irin na gurguzu bisa tushen kasuwanni. Shugaban sashen nazarin dokoki na cibiyar nazarin kimiyyar zamantakewar al'umma na kasar Sin Li Lin ya bayyana cewa,"Bayan da aka aiwatar da manufar bude kofa ga kasashen waje, kasar Sin ta kara dora muhimmanci ga tabbatar da kare hakkin jama'a. Da farko, an tabbatar da zancen rabon gado bisa kundin tsarin mulkin kasar. Amma lokacin da aka gyara kundin a shekarar 2004, an fara tabbatar da ikon dukiyar jama'a. Bayan haka, an kara tsara dokokin da suka shafi harkokin al'umma."

Ban da ba da tabbaci ga jama'a, ana maraba da jama'a da su shiga aikin tsara dokoki da gyara su. Masu nazari kan harkokin dokoki sun bayyana cewa, wannan aiki da hukumar tsara dokoki ta kasar Sin ta yi tamkar bude kofa da tsara dokoki ne. A ran 27 ga watan Satumba na shekarar 2005, an gudanar da taron sauraron ra'ayoyin jama'a kan ma'aunin biyan haraji a nan birnin Beijing, wannan ne karo na farko da majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta gudanar da taron sauraron ra'ayoyin jama'a kan tsara dokoki. Wani akanta daga lardin Jiangsu mai suna Xu Mingfu ba zai manta da wannan taro har abada ba. Ya ce,"Hukumar koli ta tsara dokoki ta kasar Sin ta saurari ra'ayoyin jama'a kai tsaye, na yi farin ciki kwarai da gaske."(Zainab)


1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China