Matsalar da Mr Chen Xu yake fuskanta ta shafi manufar ba da tabbaci ga zamantakewar al'umma. A shekarar 2010, kasar Sin ta gabatar da dokar ba da tabbaci ga zamantakewar al'umma, wadda ta zama dokar farko a fannin ba da tabbaci ga zamantakewar al'umma. Ko da yake ba a iya warware matsalar da iyayen Chen Xu suke fuskanta kai tsaye ba, amma bayan da aka aiwatar da tsarin ba da tabbaci ga zamantakewar al'umma a duk fadin kasar Sin, za a kawar da irin bambancin da ake fuskanta a tsakanin kauyuka da birane a wannan fanni.