in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na kokarin kafa cikakken tsarin kulawa da tsoffi nan da shekaru biyar masu zuwa
2011-03-09 15:43:58 cri

Sakamakon kyautatuwar ayyukan jiyya ne, aka fara samun yawan tsoffi a kasar Sin a shekara ta 1999, kuma ya zuwa karshen shekara ta 2009, yawan tsoffi na kasar Sin ya kai miliyan 167, don haka kasar ta zama ta farko a duniya mai yawan tsoffi, akwai tsoffi masu fiye da shekaru 80 da haihuwa miliyan 18.99, da kuma tsoffi nakasassu miliyan 10.36. An kiyasta cewa, ya zuwa shekara ta 2015, yawan tsoffi a kasar Sin zai kai miliyan 215, wanda zai kai kashi 15 cikin kashi dari na duk yawan mutanen kasar.

Game da wannan rukunin mutane masu dimbin yawa, Dou Yupei, mataimakin ministan harkokin jama'a na kasar Sin ya bayyana cewa, nan da shekaru biyar masu zuwa, kasar Sin za ta yi kokarin kafa wani cikakken tsarin kulawa da tsoffi. Ya kara da cewa, "yanzu muna kokarin kafa tsarin ba da hidima ga kulawa da tsoffi bisa tushen gidaje, yayin da ake dogara bisa karfin unguwoyi da hukumomin kulawa da tsoffi. Haka kuma za mu ba da tabbaci a fannonin kudi da ayyukan ba da hidima. Ta haka wannan tsari zai samu damar kafuwa bisa jagorancin gwamnatin kasar Sin da taimako daga al'ummar kasar kana da kulawar dukkan jama'ar kasar."

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China