Kawo yanzu dai, ana iya samun hukumomin ba da hidima kan kulawa da tsoffi da yawansu ya kai dubu 40 a kasar Sin, inda ake iya samun gadaje fiye da miliyan 3.12, wadanda ke daukar tsoffi da nakasassu da marayu kusan miliyan 2.37. Li Liguo, ministan harkokin jama'a na kasar Sin ya bayyana cewa, yanzu ana yada tsarin kulawa da tsoffi na kasar Sin a duk fadin kasar. Kamar yadda ya fada: "yanzu ana amfani da tsarin kulawa da tsoffi a larduna 12 daga larduna 5 a da. Sakamakon hauhawar farashin kayayyaki, ya sa aka riga a kafa tsarin ba da rangwame ga tsoffi masu fiye da shekaru 80 da haihuwa a larduna 7, a kokarin ba da tabbaci ga zaman yau da kullum na jama'a masu fama da talauci."