A halin yanzu dai, kasar Sin na gaggauta kafuwar tsare-tsaren ba da tabbaci ga zaman rayuwar nakasassu da kuma ba da hidima gare su, ta yadda za su samu tabbaci a fannonin samun jiyya da ilmi da guraban aikin yi da dai sauransu. Madam Zhang Yao ta kara da cewa, "Ya kamata al'ummarmu ta samar wa nakasassu hidimomi domin ba su tabbaci a fannin hakkinsu, a maimakon nuna musu tausayi kawai. Alal misali, ya kamata a samar musu na'urorin da za su taimaka musu, da kuma shimfida hanyoyin da suka dace da halinsu. Ta haka nakasassu za su ji dadin zaman rayuwarsu cikin mutunci."(Kande Gao)