Ana iya samun nakasassu miliyan 83 kamar Yang Jiaming a kasar Sin. Don haka, ko da yaushe gwamnatin kasar Sin ta kan dora muhimmanci kan kyautata zaman rayuwarsu, ta yadda za su iya more kyawawan sakamakon da kasar Sin ta samu ta fuskar ci gaban tattalin arziki da zaman al'umma. Daga shekara ta 2006, gwamnatin kasar Sin ta fara kebe kudi Yuan biliyan 5.71 domin kafa wani tsarin ba da tabbaci a fannin kudi da ke iya samun karuwa ba tare da tangarda ba. Ya zuwa shekara ta 2009, hukumomin ciyar da nakasassu 3471 sun ba da hidimomi ga mutane dubu 110 da kwakwalwarsu ta tabu, yayin da nakasassu fiye da miliyan 2.38 na garuruwa da gundumomi suka samu tabbaci a fannin matsayin zaman rayuwa mafi rashin tsanani, kana kuma manoma nakasassu miliyan 6.36 sun fita daga halin talauci da suka taba kasancewa ciki. A fannin sa kaimi ga samar da guraban aikin yi ga nakasassu, kasar Sin ta dauki dimbin matakai domin ba da tabbaci ga zaman rayuwarsu da kuma zaman iyalinsu. Madam Zhang Yao, wata ma'aikaciya ta sashen kula da samar da guraban aikin yi ta kungiyar kula da nakasassu ta kasar Sin ta gaya wa wakiliyarmu cewa, "kungiyar kula da nakasassu ta kasar Sin ta fitar da manufofi da matakai a jere, kamar su shirya ayyukan ba da hidima ta fuskar samun guraban aikin yi, da shirya kwasa-kwasan horaswa ta hanyoyi daban daban, da neman samar da guraban aikin yi iri daban daban ga nakasassu, kana da kara kwarin gwiwarsu wajen raya ayyukansu. Ta hanyar daukar wadannan matakai, an kyautata halin samun guraban aikin yi da nakasassu ke ciki."