Ibrahim: Bugu da kari, kayyade da kuma rage saurin raya masana'antu wadanda suke amfani da makamashi sosai kuma suke fitar da abubuwa masu gurbata muhalli kwarai shi ne muhimmin matakin da gwamnatocin wurare daban daban na kasar Sin suka dauka ta fuskar rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli. Mr. Zhu Hongren, kakakin ma'aikatar kula da masana'antu da harkokin sadarwa ta kasar Sin yana mai cewa, "Yanzu an riga an kayyade habakar wasu masana'antu masu amfani da makamashi sosai da a kan kafa su ba bisa bukatar da ake da ita ba. A cikin farkon rabin shekarar bana, yawan makamashin da manyan masana'antu suka yi amfani da shi ya ragu da kashi 1.25 cikin dari bisa makamancin lokaci na bara."
Sanusi: A ganin shehun malami Zhu Wenhui na kwalejin koyon ilmin tattalin arziki na jami'ar jama'ar kasar Sin, yin kokarin sauke nauyin rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli da yin tsimin makamashi ya bayyana yadda gwamnatin kasar Sin take da niyyar sauke nauyin da aka dora mata. Amma dole ne kasar Sin tana bukatar samun wani tsarin tsimin makamashi da rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli da za ta iya aiwatarwa cikin dogon lokaci. Shehun malami Zhu ya ce, "Yaya za a iya canza irin wannan tsari da ake gudanarwa cikin gajeren lokaci ya zama wata dokar da za a iya aiwatarwa cikin dogon lokaci na nan gaba? Ya kamata kowa ya gane cewa, raya masana'antu masu tsimin makamashi kuma marasa gurbata muhalli wani babban buri da dole ne kasar Sin ta yi kokarin cimmawa." (Sanusi Chen)