Sanusi: A shekarar 2006, lokacin da kasar Sin ta fitar da burin tsimin makamashi da rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli da take son cimmawa a shekarar bana, yawancin mutane sun dauka cewa, ba za a iya cimma wannan buri ba. Ba ma kawai kokarin tsimin makamashi da rage fitar da abubuwa masu gurbata muhallil yana shafar masana'antu ba, har ma yana shafar rayuwar jama'a ta yau da kullum. A nan birnin Beijing, matakin farko da aka dauka wajen tsimin makamashi shi ne "a kan sayi kowace fitila mai tsimin wuta a kan yuan daya". Madam Wang Yan, wata mazauniya birnin Beijing ta ce, "Wannan ce fitila mai tsimin wuta da na sanya a gidana. Unguwar da muke zaune ce ta ba mu kyauta. Mun shafe kusan shekara daya muna amfani da ita, kuma har yanzu tana aiki ba tare da wata makala ba."
Ibrahim: Bisa fitilun gargajiya da aka yi amfani da su, yawan wutar lantarki da irin wannan fitila mai tsimin wuta ke amfani da shi ya ragu da kashi 60 ko kashi 80 bisa dari, kuma tsawon lokacin da za a dauka ana amfani da ita ya ninka sau 4 zuwa 6, amma farashinta ya yi yawa, wato farashin kowace fitila mai tsimin wuta ya kai kudin Sin yuan 20 zuwa 30. Sakamakon haka, ba a son yin amfani da irin wannan fitila ba. Sabo da haka, a shekarar 2008, gwamnatin birnin Beijing ta tsai da kudurin kebe kudin tallafawa ga wadanda suke sayen irin wannan fitila mai tsimin wuta, wato za a sayi kowace fitila mai tsimin wuta a kan yuan guda kacal.