Sanusi: A hakika dai, za a iya gano cewa, kasar Sin na kokarin raya wata zaman al'umma wadda ke kokarin rage fitar da abubuwa masu dumama yanayin duniya a cikin shekaru 5 da suka gabata. Gidajen talibijin da yawa na kasar Sin su kan watsa shirye-shirye, inda ake kokarin ilmantar da jama'a hanyoyin tsimin makamashi. Wasu kamfanonin wayar salula su kan kuma aike da sakwannin da suke da nasaba da ilmin tsimin makamashi ga masu amfani da wayoyin salula.
Ibrahim: Bisa kididdigar da wata hukumar gwamnatin kasar Sin ta bayar, an ce, ya zuwa karshen 2009, biranen Beijing da Tianjin sun cimma burin tsimin makamashi kafin tsawon shekara 1 bisa shirin da aka tsara yau shekaru 5 da suka gabata. Mr. Jia Jianting, mataimakin direktan ofishin tsimin makamashi da kiyaye muhalli na kwamitin yin gyare-gyare da bunkasa birnin Beijing yana mai cewa, "Mun fi mai da hankali kan yadda za a iya yin amfani da yawancin makamashi, kuma muna kokarin sauya hanyoyin raya tattalin arziki."
Sanusi: Mr. Jia ya kara da cewa, babbar gudummawar da birnin Beijing ya bayar a fannin tsimin makamashi da rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli ita ce, kara saurin daidaita tsarin sana'o'in masana'antu.