Haka kuma, shekarar bana, shekara ce ta cika shekaru 35 da aka kulla dangantakar diplomasiyya tsakanin kasar Sin da kasashen Turai, bisa kididdigar da aka yi, an ce, a cikin shekaru 35 da suka gabata, jimillar cinikin da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Turai ta karu sau 150, kuma kungiyar EU ta zama abokin cinikayya mafi girma na kasar Sin har na shekaru 6 a jere, kuma kasar Sin ta kasance abokiyar cinikkaya ta biyu ta kungiyar EU. Hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Turai ta samu sakamako mai gamsarwa, kuma ta kawo hakikanin moriya ga jama'a da masana'antu na bangarorin biyu, Mr. Wen ya ce,"Ina fatan kasar Sin za ta bunkasa kyakkyawar dangantakar tattalin arziki da cinikayya mafi zurfi da kasashen Turai, kuma kungiyar EU ta kasance babbar kawa ce ta kasar Sin a fannin cinikayya da saka jari, ina ganin cewa, bunkasa dangantakar tattalin arziki da cinikayya dake tsakanin kasar Sin da kasashen Turai ya dace da babbar moriyar kasashen biyu da jama'arsu."
Haka kuma, firaministan Sin Mr. Wen ya ce, kasar Sin za ta ci gaba da nuna goyon baya ga farfado da tattalin arziki na kasashen Turai da warware rikicin kudi na duniya, ya ce,"Babban burinmu shi ne, mu samu daidaicin ciniki cikin dogon lokaci, ba mu samu rarar ciniki ba. A watan Janairu na bara, na ziyarci kasashen Turai, na bada kwarin gwiwa ga kasashen Turai don warware rikicin kudi na duniya, kuma na aika da tawagar kasuwanci ga kasashen Turai, don sayen kayayyaki daga kasashensu, kungiyar EU babbar kawa ce ta kasar Sin bisa manyan tsare-tsare, yayin da aka samu matsala a yankunan kasashen da ke yin amfani da kudin Euro, kasar Sin ba ta yi rikon sakainar kashi ga lamarin ba.(Bako)