Hadin gwiwa ta moriyar juna a fannonin tattalin arziki da cinikayya dake tsakanin kasashen Sin da Turai za ta samu makoma mai haske

A ranar 6 ga wata, an yi taron koli a karo na 6 kan harkokin masana'antu da kasuwanci na kasashen Sin da Turai a birnin Brussels. Firaministan Sin Mr. Wen Jiabao da shugaban majalisar tarayyar kasashen Turai Herman Van Rompuy da shugaban hukumar tarayyar Turai Jose Manuel Baroso da firaministan kasar Belgium da ke shugabancin kungiyar EU Yves Leterneb da jami'an gwamnatocin kasashen Sin da Turai da 'yan kasuwa sama da 400 sun halarci wannan taro.
Haka kuma a gun taron, Mr. Wen ya yi jawabi, inda ya waiwayi baya game da hadin gwiwa ta fuskar tattalin arziki da cinikayya dake tsakanin kasashen Sin da Turai bayan da aka kulla dangantakar diplomasiyya a tsakaninsu, kuma jawabin da ya yi ya samu karbuwa sosai.
1 2 3