in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hadin gwiwa ta moriyar juna a fannonin tattalin arziki da cinikayya dake tsakanin kasashen Sin da Turai za ta samu makoma mai haske
2010-10-07 18:33:15 cri

An yi taron ne, yayin da tattalin arziki na kasashen duniya ya samu farfadowa, kuma ba a kawar da mummunan tasirin da rikicin kudi ya haifar ba, kuma har zuwa yanzu dai tana kasa tana dabo wajen farfado da tattalin arziki na duniya. A karkashin wannan yanayi, 'yan kasuwa da masu masana'antu na kasar Sin da na kasashen Turai sun yi hadin gwiwa tare, domin tattaunawa fannonin tattalin arziki da cinikayya dake tsakanin kasar Sin da kasashen Turai, kuma wannan na da ma'ana ta musamman ga farfado da tattalin arziki na duniya, da ingiza aikin bunkasa tattalin arziki na duniya yadda ya kamata kuma cikin dogon lokaci. A cikin jawabin da Mr. Wen ya yi, ya ce, a cikin 'yan shekarun nan, cinikin da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Turai ya bunkasa cikin hanzari, musamman ma, a cikin shekaru 2 da suka gabata, watau, yayin da ake fama da rikicin kudi na duniya, yawan kayayyakin da kungiyar EU ta fitar ga kasar Sin ya ci gaba da karuwa, ya ce, "gaskiya ne cewa, cinikin da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Turai da yawan jarin da aka zuba sun bunkasa cikin hanzari. Bisa kididdigar kungiyar EU, an ce, a shekara ta 2008 da 2009, yayin da aka samu rikicin kudi na duniya, yawan kayayyakin da kungiyar EU ta fitar ga kasashen duniya ya ragu, amma yawan kayayyakin da ta fitar ga kasar Sin ya karu da kashi 4 cikin 100. Kana kuma, a farkon rabin shekarar bana, yawan kayayyakin da kungiyar EU ta fitar ga kasar Sin ya karu da kashi 42 cikin 100."

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China