in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gano kasar Kenya
2010-09-17 16:21:44 cri

Kamar yadda Mr. Otieno O. Maurice ya bayyana, nune-nune masu siffar musamman na nahiyar Afrika da rumfar kasar Kenya ta yi sun jawo hankalin masu yawon shakatawa na kasar Sin da na sauran kasashen duniya, kuma wasu daga cikinsu sun dauki hotuna tare da samfur na namun daji da halittu. Mr. Wang, wani mai yawon shakatawa ne da ya fito daga lardin Sichuan na kasar Sin yana daya daga cikin wadannan masu yawon shakatawa, ya ce, "A ganina, nune-nunen da rumfar kasar Kenya ta gabatar sun bayyana hakikanin yanayi na zaman rayuwar jama'ar kasashen Afrika, kayayyakin da aka gabatar a cikin rumfar suna da ma'ana sosai a fannin al'adu. Ina son wannan rumfa sosai, kayayyakin wasan fasaha da suka kawo wa kasar Sin kayayyaki ne masu daraja na kasar Kenya."

Ban da hotuna masu dimbin yawa da raye-raye da wake-wake masu ban sha'awa da aka nuna a cikin rumfar, kayayyakin musamman sun jawo hankalin masu yawon shakatawa domin dandanawa da saya. Daga cikin wadannan kayayyaki, kofin kasar Kenya ya fi samun karbuwa.

Rumfar kasar Kenya tana bude kofa ga duk wanda ke da sha'awa ga al'adun Afrika da kyakkyawar surar kasar Kenya, ba shakka, za a shirya muku raye-raye da wake-wake masu ban sha'awa da nune-nune iri daban daban da kofi mai dadin sha.(Lami)


1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China