in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gano kasar Kenya
2010-09-17 16:21:44 cri

Rumfar kasar Kenya tana cikin babbar hadaddiyar rumfar kasashen Afrika dake shiyyar C ta farfajiyar bikin EXPO na Shanghai, inda aka yi nune-nune domin gabatar da tsarin neman samun bunkasuwa mai dorewa da kyakkyawar hulda a tsakanin muhallin halittu da bil Adam ta kasar Kenya, ban da haka kuma, an gabatar da kalubalen da kasar Kenya take fuskanta wajen bunkasa birane. An raba rumfar kasar Kenya zuwa yankuna guda 4 ciki har da "Kauyuka" wato "Manyatta" da "lambun shan iska na kasar" da "sabon birnin Nairobi" da kuma "tsohon birnin Lamu". Shugaban rumfar kasar Kenya Otieno O. Maurice ya bayyana cewa, "Da farko, mun bude kofar yankin nune-nune na 'tsohon birnin Lamu', daga bisani, mun gabatar da yankin nune-nune na birnin Mombasa wanda wani shahararren birni ne a fannin yawon shakatawa na kasar. Sannan kuma, mun gabatar da yankin nune-nune na birnin Nairobi domin bayyana muhimmiyar rawa da wannan birni ya taka a fannin tattalin arziki da yankin tsakiya da gabashin nahiyar Afrika."

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China