Dangane da haka, madam Wang Li, mataimakiyar shugaban sashen tuntubar kasashen waje na kwamitin sa kaimi kan harkokin ciniki na kasar Sin kuma babbar sakatariyar hukumar harkokin masana'antu da kasuwanci tsakanin kasashen Sin da Afirka ita ma ta nuna amincewa. A yayin taron tattaunawar da aka yi a ran 26 ga wata, madam Wang ta bayyana cewa, a matsayinsa na kwamiti mafi girma a nan kasar Sin a fannin sa kaimi kan harkokin ciniki da zuba jari, ko da yaushe kwamitin na sa himma wajen sa kaimi kan bunkasa dangantakar tattalin arziki da ciniki a tsakanin Sin da kasahen waje, ciki har da kasashen Afirka, ta kuma nuna karfin zuciya kan makomar yin hadin gwiwa a tsakanin kasashen Sin da Botswana. Madam Wang tana mai cewar,"Kwamitinmu na sa kaimi kan harkokin ciniki kuma muna son taka rawa a matsayin wani dandalin hada kan hukumomin harkokin masana'antu da kasuwanci. Za mu hada kai da takwarorinmu na Botswana, a kokarin taimakawa masana'antun kasashen 2 wajen kara fahimtar juna da yin hadin gwiwa ta hanyoyin shirya tattaunawa da tarurukan tsakanin masana'antu tare da kafa kungiyoyin wakilai domin kai wa juna ziyara da dai sauransu."
Kwamitin sa kaimi kan harkokin ciniki na kasar Sin da ofishin jadakancin kasar Botswana a nan kasar Sin su ne suka shirya wannan taron tattaunawa, inda jami'ai da kwararru da masu masana'antu kimanin dari 2 suka hallarci wannan dandali. (Tasallah)