in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Sin da Botswana sun tattauna kan harkokin ciniki da tattalin arziki
2010-09-15 20:07:47 cri

A game da wannan, madam Dorcus Makgato-Malesu, ministar ciniki da masana'antu ta Botswana ta nuna amincewa matuka, inda ta ce,"Masana'antun kasar Sin suna gudanar da manyan ayyukan jin dadin jama'a a kasarmu ta Botswana, kamar gina gadoji da madatsar ruwa da gidaje da dai sauransu. Baya ga yin hadin gwiwa a harkokin kasuwanci a tsakanin kasarmu da Sin, kasar Sin ta taka rawa sosai wajen raya ayyukan jin dadin al'umma a kasarmu ta hanyar ba da kyautar kudi da dai makamantansu."

Duk da haka, ko da yake Sin da Botswana sun samu saurin ci gaban dangantakar tattalin arziki da ciniki a shekarun baya, amma a ganin madam Makgato-Malesu, ciniki da zuba jari ba su bunkasa sosai a tsakanin Botswana da Sin ba, suna da kyakkyawar makoma wajen yin hadin gwiwa a nan gaba, inda ta ce,"A ganina, ya kamata mu yi kokarin wajen shirya tattaunawa domin tabbatar da sauyi irin na wannan hali. Ina fatan hukumomin dake kula da kasuwanci na Botswana da Sin za su hada kai, za su yi mu'amala da ziyartar juna da kuma yin amfani da bayanan tattalin arziki da ciniki tare, tabbas hakan zai taimakawa wajen kara yawan kudin ciniki da zuba jari a tsakanin kasashen 2."

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China