Kasashen Sin da Botswana sun kulla dangantakar diplomasiyya a shekarar 1975. A cikin shekaru 35 da suka wuce, kasashen 2 sun raya dangantakarsu yadda ya kamata, suna ta yin mu'amala ta fagen ciniki da tattalin arziki. Ya zuwa karshen shekarar 2009, kasar Sin ta zuba dalar Amurka biliyan 735.3 a Botswana kai tsaye. Sa'an nan kuma, masana'antun kasar Sin sun taka rawa a ayyukan gine-gine a Botswana, suna ba da gudummawa sosai wajen kyautata ayyukan jin dadin jama'a da ma fasahohi a wurin.