in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An shirya taron kara wa juna sani kan matakan samun bunkasuwa tsakanin Sin da kasashen Afrika
2010-09-15 17:14:30 cri

Dadin dadawa, Chong Quan ya ce, bankin duniya ya kafa wasu yankunan masana'antu a kasashen Afrika, kasar Sin kuma tana kokarin taimakawa kasashen Afrika wajen kafa yankunan hadin kai na tattalin arziki da cinikayya, da kuma yankunan bude kofa ga kasashen ketare, ya yi fatan manufofin da kasar Sin ke aiwatarwa game da kafa yankunan musamman na tattalin arziki za su taka rawa wajen samun bunkasuwar kasashen Afrika.

Manyan jami'ai da suka fito daga kasashen Afrika guda goma, ciki har da Nijeriya, Ghana, Kenya da sauransu, da jami'an ofishin jakadanci na kasashen ketare dake nan kasar Sin, da manyan wakilai na bankin duniya, da kuma wakilai na ma'aikatu daban daban na kasar Sin, wadanda yawansu ya wuce 100 ne suka halarci taron.(Bilkisu)


1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China