A cikin jawabinsa, mataimakin ministan kudi na kasar Sin, Wang Jun ya nuna cewa, 'A cikin shekaru fiye da 30 da suka wuce bayan aiwatar da manufar yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen ketare, kasar Sin ta samu babbar nasara a fannoni daban daban. Wannan ya nuna cewa, a yayin da ake kokarin yin tsayin daka kan samun 'yancin kai, da aiwatar da harkoki na cin gashin kai, kamata ya yi a kara kokarin samun bunkasuwar tattalin arzikin duniya kuma ya zamo bai daya. Ya kamata a nemi wata hanyar bunkasuwa bisa yanayin da kasar ke ciki, da kuma inganta samun sakamako mai kyau a nan gaba ta hanyar yin gyare-gyare. Muna son gabatar da fasahohin da muka mallaka wajen samun bunkasuwa ga kasashe daban daban na Afrika.'