in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An shirya taron kara wa juna sani kan matakan samun bunkasuwa tsakanin Sin da kasashen Afrika
2010-09-15 17:14:30 cri

Bayan haka kuma, Wang Jun ya bayyana cewa, kasar Sin da bankin duniya za su sa himma domin karfafa hadin kai tsakaninsu da kasashen Afrika. Shugaban bankin duniya Robert B. Zoelick ya nuna yabo ga taron kara wa juna sani kan matakan samun bunkasuwa a tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika. Ya nuna cewa, 'Hadin gwiwar da ake yi tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika a fannin cinikayya yana da dogon tarihi. A 'yan shekarun da suka wuce, jimillar kudin da kasar Sin da kasashen Afrika suke samu wajen yin cinikayya tana karuwa da kashi 40 cikin dari a ko wace shekara. Fasahohin da kasar Sin ta samu wajen bunkasuwa za su taimaka wa kasashen Afrika a fannonin fama da talauci da samun karuwar tattalin arziki.'

A yayin da ake magana kan fasahohin taimakawa samun bunkasuwa da kasar Sin ta mallaka a cikin gajeren lokaci, wani jami'i na ma'aikatar cinikayya ta kasar Sin Chong Quan ya bayyana cewa, kasar Sin da kasashen Afrika dukkansu kasashe ne masu tasowa, shi ya sa kasashen Afrika na iya koyon fasahohin da Sin ta samu wajen aiwatar da manufar yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen ketare. Chong Quan ya kara da cewa, 'Kasashe masu tasowa suna cikin yanayi iri daya, koyon fasahohin bunkasuwa tare a tsakaninsu na da ma'ana sosai wajen kara gogewarsu ta neman bunkasuwa da kansu. Saboda haka, shirya taron kara wa juna sani tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika ya dace da hakikanin halin da bangarorin biyu ke ciki, har da ma bukatunsu.'

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China