in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bikin EXPO na Shanghai ya samar wa 'yan jarida hidima mai kyau
2010-08-24 17:33:11 cri


Zhang Yulong, wani 'dan jarida dake halartar bikin baje koli na Shanghai ya gaya mana cewa, cibiyar watsa labaru ta kan aika motocin musamman ga 'yan jarida, a lokacin da yanayi ya haura digiri 40 na sentigred, an canja tashar motocin musamman kusa da shingen tsaro. Lallai, ana bai wa 'yan jarida hidima mai kyau a dukkan fannoni.

Bayan haka kuma, an ajiye wata kujerar tausa a ko wane dakin aiki don kula da lafiyar 'yan jarida.

Tun daga ranar da aka soma yin gwajin aiwatar da harkokin bikin baje koli na duniya na Shanghai a kwanaki 120 da suka wuce har zuwa yanzu, daga aikin tsara takardun shaida fiye da dubu goma, zuwa aika motocin musamman ga 'yan jarida, daga kyautata yanayin cin abinci zuwa kafa na'urorin rage tasirin hasken rana, dukkan ayyukan sun sanya cibiyar watsa labaru ta bikin EXPO na Shanghai ta zama tamkar gidan 'yan jarida.
1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China