in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bikin EXPO na Shanghai ya samar wa 'yan jarida hidima mai kyau
2010-08-24 17:33:11 cri

Kusan watanni hudu da suka wuce bayan bude bikin baje koli na duniya na Shanghai, bisa kididdigar da aka yi an ce, yawan 'yan jarida da suka yi rajista don shiga farfajiyar bikin ya kai kusan dubu 130, wadanda suka fito daga kasashen ketare kuma sun wuce dubu 10.

Ya zuwa karshen watan Yuli na bana, an shirya tarurrukan manema labaru fiye da 100 a cibiyar watsa labaru ta bikin baje koli. Bayan haka, cibiyar watsa labaru ta tsara shirye-shirye na tsawon awoyi 260. Kungiyar watsa labaru ta gwamnatin kasar game da bikin kuma ta samar da shirye-shirye ta talibjin na tsawon mintoci dubu 2.7. A matsayinsa na kamfanin dillancin labaru mai masaukin baki a bikin EXPO, kamfanin dillancin labaru na Xinhua ya gabatar da hotuna ga kafofin watsa labaru sama da 100 da suka fito daga kasashe masu tasowa.

Wani jami'i na gidan talibijin na kasar Jamus ya gaya mana cewa, daga ranar 26 zuwa 30 ga watan Afrilu bayan bude bikin baje koli na duniya na Shanghai, yawan mutanen da suka kalli shirye-shirye a jere da gidan talibijinsu ya tsara game da bikin kan kai kashi 21.6 cikin dari a ko wace rana, wato akwai mutanen da yawansu ya kai kimanin miliyan 5 da suke kallon shirye-shirye na wannan talibijin a ko wace rana. Wannan jami'i ya ce, sun samu wannan kyakkyawan sakamako ne a karkashin goyon baya da bangaren kasar Sin ke bayarwa a fannonin gabatar da na'urorin watsa labaru kai tsaye, da na tsara shirye-shirye.
1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China