Sanusi: Lokacin da kasar Sin take cika alkawuranta, tana kuma samun moriyar yin cinikayya cikin 'yanci. Shehun malami He Weiwen ya kara da cewa, sabo da mambobin kungiyar WTO suna bude wa juna kasuwanninsu, yawan kayayyakin da kasar Sin ke fitarwa da shigowa ya samu karuwa sosai.
Ibrahim: Sabo da haka, yanzu muna iya fadin cewa, kasar Sin ta riga ta cika alkawuran da ta dauka kafin a shigarta cikin kungiyar WTO, ba ma kawai wannan wata muhimmiyar alama ce ba, har ma ya kasance wani muhimmin lokaci ne ga kasar Sin. A nan gaba, ya kamata kasar Sin ta kara daukar nauyin da ya rataya a wuyanta wajen bunkasa cinikayya cikin 'yanci. (Sanusi Chen)