in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta cika alkawuran da ta dauka lokacin da aka shigarta cikin kungiyar WTO
2010-08-19 21:30:42 cri

Sanusi: A cikin alkawarin da kasar Sin ta dauka kafin shigarta cikin kungiyar WTO, batun rage katangar cinikin waje wani muhimmin alkawari ne da ya fi jawo hankalin mutane. Game da yadda kasar Sin ta cika wannan alkawari, shehun malami He Weiwen ya bayyana cewa, "Bisa alkawarin da kasar Sin ta dauka, matsakacin yawan harajin kwastam da kasar Sin ta samu ya kai kimanin kashi 10 cikin dari, amma yanzu wannan adadi bai kai kashi 10 cikin kashi dari ba. Matsakaicin yawan harajin kwastam da ake sanyawa kayayyakin masana'antu ya kai kashi 9 cikin kashi dari, sannan matsakaicin harajin kwastam da ake sanyawa amfanin gona ya kai kashi 15 cikin kashi dari. Akwai bambancin da yake kasancewa a tsakanin kayayyaki daban daban. Kasar Sin ta cika wannan alkawari ne a karshen shekarar 2006."

Ibrahim: Kafin a shigar da kasar Sin cikin kungiyar WTO, wasu mutanen kasar Sin sun nuna damuwa ga matakin rage harajin kwastam. Wasu sun dauka cewa, matakin rage haraji zai matsa wa masana'antun kasar Sin lamba, kuma zai kawo illa ga tattalin arzikin kasar. Amma al'amarin ba haka yake ba. A lokacin da ake tinkarar matsalar hada-hadar kudi a duniya, saurin karuwar tattalin arzikin kasar Sin ya kai kashi 8.7 cikin kashi dari a shekarar 2009. Game da wannan, shehun malami He Weiwen ya yi nazarin cewa, "Akwai dalilai guda biyu. Da farko dai, yanzu tattalin arzikin kasar Sin yana samun ci gaba kamar na sauran kasashen duniya. Kuma yawan kayayyakin da take fitarwa da kuma shigo da su ya karu. Sakamakon haka, yanzu kasar Sin ta riga ta saba da tasirin da kasuwannin kasashen duniya suke yi mata. Sannan, bayan da aka rage harajin kwastam da ake sanyawa kayayyakin da ake shigowa da su, masana'antun kasar Sin sun bunkasa sosai wajen yin takara a kasuwa. Wannan matakin rage harajin kwastam ya yi kyakkyawan tasiri ga masana'antun kasar Sin."

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China