Sanusi: A kwanan baya, lokacin da yake yin hira da wakilin gidan talibijin na Phoenix na yankin Hongkong na kasar Sin, Mr. Pascal Lamy, babban direktan kungiyar WTO ya bayyana cewa, "Kasar Sin tana da muhimmanci sosai ga kungiyar WTO, yanzu tana taka muhimmiyar rawa a lokacin da ake raya cinikayya a tsakanin kasa da kasa, kuma ta riga ta cika alkawuran da ta dauka lokacin da aka shigarta cikin kungiyar WTO."
Ibrahim: A cikin wata sanarwar da ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta bayar a karshen watan Yuli, an nuna cewa, ya zuwa shekarar 2010, kasar Sin ta cika dukkan alkawuran da ta dauka lokacin da aka shigarta cikin kungiyar WTO, sannan ta kafa tsarin tattalin arziki da cinikayya da yake dacewa da ka'idojin kungiyar WTO. Sakamakon haka, yanzu kasar Sin ta zama daya daga cikin kasuwannin da suka fi bude kofa ga sauran kasashen duniya. Shehun malami. He Weiwen wanda yake nazarin harkokin cinikayyar da ke gudana tsakanin kasar Sin da kasar Amurka ya bayyana cewa, "Bisa wasu bayanan da muka samu, za mu iya ganewa ko kasar Sin ta cika alkawuranta ko a'a. Da farko dai, game da amfanin gona, kasar Sin ta taba daukar alkawarin cewa, ya zuwa shekarar 2010, harajin kwastam da za ta sanya kan amfanin gona da ake shigo da su daga kasashen waje ya ragu sai ya kai kashi 15 cikin dari. Yanzu kasar Sin ta cika wannan alkawari. Haka kuma, lokacin da aka shigarta cikin kungiyar WTO, ta riga ta soke tallafin kudin da take kebe wa kamfanoni wadanda suke fitar da amfanin gona zuwa kasashen waje."