in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bikin ranar rumfar kasar Nijeriya a gun bikin EXPO na Shanghai zai nuna al'adu masu yawa da suka bunbanta da juna
2010-08-19 14:54:09 cri

Nijeriya kasa ce dake da tattalin arziki mafi girma na biyu da ke kudancin hamadar Sahara, kasar tana son yin amfani da damar shiga bikin EXPO wajen kara yin hadin gwiwa a fannin tattalin arziki da ciniki tare da kasar Sin. Sabo da haka, bayan bikin ranar rumfar kasar Nijeriya a gun bikin EXPO, kasar za ta shirya ranar yin ciniki da zuba jari da ke tsakanin Sin da kasar Nijeriya. "A ran 22 ga wata, za mu shirya bikin ranar yin ciniki da zuba jari da ke tsakanin Sin da kasar Nijeriya, kamfanoni masu son yin ciniki da hadin gwiwa tare da kamfanonin kasar Sin za su shiga wannan bikin, a gun bikin, wadannan kamfanoni za su iya yi mu'amala da yin ciniki, ina fatan masu ciniki na kasashen biyu za su kara yin hadin gwiwa a fannonin yin ciniki da zuba jari."

Game da yin ciniki da ke tsakanin kasar Nijeriya da kasar Sin, Jubrili Martins-Kuye ya bayyana cewa, aikin yin hadin gwiwa da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka zai kawo moriya ga kasashen Afirka.Kuma ya kara da cewa, "A ganinna, tun daga 'yan shekaru da suka wuce zuwa yanzu, kasar Sin tana yin kokari wajen zama abokiya kasashen Afirka, da yin hadin gwiwa tare da kasashen Afirka, musamman ma, kasar Sin tana yin kokari wajen yin hadin gwiwa tare da kasar Nijeriya, don sa kaimi ga yunkurin shimfida tsarin masana'antu na Nijeriya. Kasar Sin tana da sha'awar zuba jari ga masana'antu, kuma Sin tana ba da taimako ga kasar Nijeirya a fannin gina manyan ayyukan yau da kullum, kasar Nijeirya ta samu moriya daga yin hadin gwiwa tare da kasar Sin." (Abubakar)


1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China