in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bikin ranar rumfar kasar Nijeriya a gun bikin EXPO na Shanghai zai nuna al'adu masu yawa da suka bunbanta da juna
2010-08-19 14:54:09 cri

A ran 21 ga wata, za a yi bikin ranar rumfar kasar Nijeriya a gun bikin EXPO da ke gudana a birnin Shanghai na kasar Sin, game da batun yadda kasar Nijeriya ta yi amfani da damar halarta bikin EXPO wajen yin mu'amala tare da kasar Sin, a ran 17 ga wata, manemi labaru na gidan rediyon kasar Sin ya samu labaru daga ministan ma'aikatar masana'antu da cinikayya na kasar Nijeriya Jubril Martins-Kuye.

Ma'aikatar masana'antu da cinikayya ita ce ta shirya rumfar kasar Nijeriya a gun bikin EXPOna Shanghai, kuma a ran 21 ga wata, Jubril Martins-Kuye zai isa birnin Shanghai don halartar bikin da za a yi. Game da babban jigon bikin EXPO "birni mai kayatarwa da kuma zaman rayuwa mai inganci", Jubril Martins-Kuye ya bayyana cewa, "Wannan jigo ya shaida cewar kasar Sin tana fatan za a iya inganta zaman rayuwar jama'a a duniya, a sa'i daya kuma, kasar tana fatan za a bunkasa birane na duniya kamar yadda ya kamata".

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China