in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Madam Tchakanhuhen wadda ke sayar da busasshen nama
2010-08-17 16:34:17 cri

Sanusi: Madam Tchakanhuhen ta yi bakin ciki sosai sakamakon damuwa da matsalolin da take fuskanta. Lokacin da take cikin irin wannan mawuyacin hali, ta samu labarin cewa, hukumar kula da harkokin neman aikin yi ta gundumarsu ta bude wani kwas domin makiyaya wadanda suka yi watsi da sana'arsu ta gargajiya, kuma suke rayuwa a cikin gari. Sabo da haka, madam Tchakanhuhen ta shiga wannan kwas ta soma koyon ilmin zamani na yin kasuwanci. Ta soma fahimtar hanyar yin kasuwanci sannu a hankali. Sabili da haka, ta soma tafiyar da kantin sayar da busasshen nama kamar yadda ya kamata. Madam Tchakanhuhen ta bayyana cewa, "Lokacin da na bude wannan kanti, ban iya tafiyar da shi kamar yadda ake fata ba, amma tun daga shekarar 2009, yawan kudin da na samu ya karu. Ka ga wadannan na'urorin sanyayya kayayyaki 7. Da farko, na sayi wani karami, sannan daga baya na soma sayen masu girma. Har ma na sayi na'urar sanyayya daki a bana. Haka kuma, a da na sayi busasshen nama kadan daga hannun sauran mutane, amma yanzu ina sayen busasshen nama da yawa a kowane lokaci nake bukata. Yawan kudin da na iya samu yanzu ya kai dubban kudin Sin yuan a kowace rana."

Ibrahim: Lokacin da kananan 'yan kasuwa kamar madam Tchakanhuhen suke kasuwanci, gwamnatin wurin ta dauki jerin kyawawan matakan da suke da nasaba da fasaha da tallafin kudi da haraji da dai sauransu domin nuna goyon baya ga makiyaya da su yi kasuwanci. Madam Tchakanhuhen ta ce, "A hakika dai, gwamnati ta aiwatar da wasu kyawawan manufofi, kuma ba mu bukatar biyan kudin yin kasuwanci da na haraji. A farkon shekarar bude wannan kanti a shekarar 2009, na shiga wani kwas da hukumar kula da harkokin samar da aikin yi ta shirya ba tare da biya ko da kobo daya ba. Har ma na samu rancen kudin da yawansa ya kai kudin Sin yuan dubu 20, ko da yake ya yi kadan, amma na yi amfani da wadannan kudade domin kara girman kantina a kasuwa."

Sanusi: Madam Tchakanhuhen ta tuna da cewa, lokacin da ita da iyalinta suka yi kiwon dabbobi a filin ciyayi, yawan kudin shiga da suka samu ya kai kudin Sin yuan kimanin dubu 40 a kowace shekara, amma yanzu wannan adadi ya kai fiye da kudin Sin yuan dubu dari 1. (Sanusi Chen)


1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China