"Bayan da muka kaura daga garinmu zuwa wannan garin, sai na yanke shawarar neman aikin yi. Na ga cewa bude wani kantin sayar da kayayyakin da ake yi a garinmu hanya ce mai kyau da ta dace da mu. Ina ganin za a samu kudi. Sabo da haka, bayan na samu kudin tallafin da gwamnati ta ba mu, sai na sayi wannan kanti ba tare da bata lokaci ba, kuma na zuba dukkan kudina a wannan kanti."
Ibrahim: Ko da yake madam Tchakanhuhen ta yi namijin kokari wajen tafiyar da kanti, amma da farko, wasu azzatumen 'yan kasuwa su kan yaudare ta, kuma ta fuskanci wahaloli sosai. Madam Tchakanhuhen ta gane cewa, babu saukin rayuwa a cikin gari. Ta bayyana cewa, "Lokacin da muka iso wannan gari, na ga cewa akwai kyakkyawan muhalli a nan. Amma daga baya, sai na fahimta cewa halin da ake ciki a garin yana da sarkakiya. Ba mu da ilmi da fasahar yin kasuwanci, a kan yaudare mu."