Sanusi: Tun daga karshen shekara ta 2007, aka soma daukar matakin hana kiwon dabbobi a filayen ciyayi na garin da madam Tchakanhuhen take zaune, da kuma na komar da makiyaya garuruwa. Sakamakon haka, madam Tchakanhuhen ta sayar da dukkan tumaki dari 4 da ta mallaka, kana ta koma wani gari da zama tare da iyalinta 5. Su makiyaya ne, sabo da haka, yaya za su yi rayuwa a cikin gari? Madam Tchakanhuhen ta kan yi nazarin wannan al'amari matuka, kuma ta kan yi bincike a kasuwa. Daga karshe dai, ta sami wata hanyar neman kudin da za ta tafiyar da rayuwarta, wato sayar da busasshen nama. Sabo da haka, ta yi amfani da kudin tallafin da yawansa ya kai kudin Sin yuan dubu 30 da gwamnatin wurin ta samar musu domin bude wani kantin sayar da busasshen nama da kayayyakin da aka yi da madara a farkon shekarar 2008.