in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Equatorial Guinea ya halarci bikin ranar rumfar kasar a gun bikin EXPO na Shanghai
2010-08-17 14:23:52 cri

Shugaban babbar hukumar kwastan ta kasar Sin Sheng Guangzu ya halarci bikin ranar rumfar kasar Equatorial Guinea na bikin EXPO na birnin Shanghai, inda ya bayyana cewa, tun daga shekaru 40 da suka wuce da kafuwar dangantakar diplomasiyya da ke tsakanin kasashen biyu zuwa yanzu, kasashen biyu sun bunkasa dangantakar da ke tsakaninsu kamar yadda ya kamata, jama'ar kasashen biyu suna zaman abokan arziki, kuma suna zaman daidai wa daida da ba da taimako ga juna.

A gun bikin, malam Sheng Guangzu ya bayyana cewa, kasar Equatorial Guinea ita muhimmiyar kasa a gulf Guinea. A cikin rumfar kasar Equatorial Guinea na bikin EXPO, ba ma kawai a iya duba kyan ganin kasar, har ma a iya ganin kokarin da jama'ar kasar Equatorial Guinea suka yi wajen kiyaye muhalli.

Ban da haka kuma, a gun bikin rumfar ranar kasar Equatorial Guinea na bikin EXPO, kungiyar kide-kide da wake-wake na kasar ta yi wake-wake da raye-raye.(Abubakar)


1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China