in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Equatorial Guinea ya halarci bikin ranar rumfar kasar a gun bikin EXPO na Shanghai
2010-08-17 14:23:52 cri

A ran 16 ga wata, shugaban kasar Equatorial Guinea Teodoro Obiang Nguema Mbasogo ya halarci bikin ranar rumfar kasarsa a gun bikin EXPO da ke gudana birnin Shanghai, a gun bikin, a madadin gwamnati da jama'ar kasar Teodoro Obiang Nguema Mbasogo ya nuna alhini sosai ga mutanen wadanda suka mutu a sakamakon fama da bala'in gangarowar duwatsu da laka a gundumar Zhouqu na lardin Gansu na kasar Sin.

A gun bikin, malam Teodoro Obiang Nguema Mbasogo ya bayyana cewa, bala'in gangarowar duwatsu da laka a gundumar Zhouqu ya yi sanadiyar hasarar rayuka da dukiya sosai, kasar Equatorial Guinea ta nuna jejeto cikin sahihiyar zuciya ga gwamnatin kasar Sin da jama'ar kasar, kuma ya yi imani cewa, jama'ar kasar Sin za su iya farfado da gundumar Zhouqu cikin sauri.

Sabo da an yi zaman makoki a kasar Sin ga wadanda suka rasu sakamakon bala'in zaizayewar kasa a Zhouqu, an jinkirtar da lokacin bikin ranar rumfar kasar Equatorial Guinea a gun bikin EXPO na birnin Shanghai, ta haka, an shirya bikin ranar rumfar kasar a ran 16 ga wata.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China