in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Equatorial Guinea ya halarci bikin ranar rumfar kasar a gun bikin EXPO na Shanghai
2010-08-17 14:23:52 cri

A gun bikin, malam Teodoro Obiang Nguema Mbasogo ya kara da cewa, bikin EXPO da gwamnatin kasar Sin ta shirya a birnin Shanghai, wannan ya bayyana babbar aniyar kasar Sin wajen gudanar da manufar bude kofa ga kasashen ketare, kuma wannan biki zai kawo moriya ga kasashe masu tasowa wajen koyi da sakamakon da kasashe masu ci gaban masana'antu suka samu, da kara fahimtar juna tsakanin kasashe daban daban.

Ban da haka kuma, malam Teodoro Obiang Nguema Mbasogo ya bayyana cewa, tun daga shekaru 10 da suka wuce zuwa yanzu, gwamnatin kasar Equatorial Guinea ta yi kokari wajen bunkasa tattalin arzikin kasar, a ganin gwamnatin kasar, ba ma kawai kasar ta samu bunkasuwa sosai, har ma ta ba da gudumawa ga kasashen duniya. Kuma a 'yan shekaru da suka wuce, kamfanonin kasar Sin sun ba da taimako ga kasar wajen gina manyan ayyukan yau da kullum.

A gun bikin EXPO da ake shirya a birnin Shanghai, ra'ayin da kasar Equatorial Guinea ta gabatar shi ne "bunkasa birane masu dorewa", kuma a ganin kasar, ya kamata a kafa tsarin kiyaye muhalli yayin da bunkasa birane.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China