in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi biki a ranar rumfar kasar Gabon a gun bikin EXPO na Shanghai
2010-08-05 16:40:37 cri

A cikin jawabin da firayim ministan kasar Gabon Paul Biyoghe Mba ya yi, ya nuna godiya ga taimakon da gwamnatin kasar Sin ta samar wa Gabon wajen shiga bikin EXPO. Inda ya bayyana cewa, "A watan Oktoba na shekarar 2006, kafin kaddamar taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin kai a tsakanin Sin da kasashen Afirka, tawagar kasar Gabon da ke karkashin jagorancin tsohon shugaban kasar El Hadj Omar Bongo Ondimba ta kai ziyara a birnin Shanghai. A yayin ziyarar, tsohon shugaban kasar ya je don ganewa idonsa wurin da ake ginawa don bikin EXPO. El Hadj Omar Bongo Ondimba shi ne shugaban wata kasar waje na farko wajen kulla yarjejeniyar shiga bikin EXPO. Ya nuna goyon baya sosai ga kasar Gabon da ta shiga bikin EXPO na birnin Shanghai domin kasashen Sin da Gabon suna da dankon zumunci a tsakaninsu. Kuma tare da fatan a yi nasara wajen gudanar da bikin murnar ranar rumfar Gabon."

Rumfar Gabon a bikin EXPO na birnin Shanghai ta yi amfani da aikin kiyaye muhalli don nuna albarkatun dazuzzuka. A cikin rumfar, akwai sassan 3 wato sashen ci gaban kyauyuka da sashen bunkasuwar birane da sashen albarkatun dazuzzuka. Wani jami'in rumfar Gabon a bikin EXPO na birnin Shanghai Ludovic MBA ya bayyana wa manema labaru cewa, rumfar Gabon ta kan jawo hankalin masu yawon shakatawa da yawa a ko wace rana. Kuma ya bayyana cewa, "bisa kididdigar da muke yi, yawan mutane masu yawon shakatawa da suka shiga rumfar Gabon kan kai a kalla dubu 10 a ko wace rana. Kuma a wasu lokata, yawan mutanen da suka yi yawon shakatawa a rumfar Gabon kan wuce dubu 20. Na yi imani cewa, a 'yan kwanaki masu zuwa, yawan mutanen da za su yi yawon shakatawa a rumfar zai karu sosai."


1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China