in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi biki a ranar rumfar kasar Gabon a gun bikin EXPO na Shanghai
2010-08-05 16:40:37 cri

A kwanan baya, an yi bikin murnar ranar rumfar kasar Gabon a bikin EXPO da ake gudanarwa a birnin Shanghai na kasar Sin. Firayim ministan kasar Gabon Paul Biyoghe MBA da ministan kiwon lafiya na kasar Sin, Chen Zhu sun halarci bikin murnar ranar tare da yin jawabai.

Da farko, malam Chen Zhu ya nuna babban yabo ga ra'ayin hada birane da kyauyuka da rumfar Gabon ta nuna a gun bikin EXPO na Shanghai. Kuma ya bayyana cewa, rumfar kasar Gabon ta bayyana gudummawar da jama'ar kasar suka ba da wajen bunkasa kasarsu tare da zaman al'umma mai jituwa a fannonin gine-gine da ayyukan kawo albarka da zirga-zirga da al'adun kasar da aikin kiyaye muhalli.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China