in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi biki a ranar rumfar kasar Gabon a gun bikin EXPO na Shanghai
2010-08-05 16:40:37 cri

Malam Chen Zhu ya bayyana cewa: " bikin murnar ranar rumfar kasar Gabon ya ba mu wata dama wajen fahimtar al'adun kasar Gabon da wurare masu ban sha'awa na kasar."

Ban da haka kuma, malam Chen Zhu ya jaddada dankon zumunci da ke tsakanin kasashen biyu. Inda ya bayyana cewa, " tun shekaru 36 da suka wuce da kafa dangantakar diplomasiyya a tsakanin kasashen biyu zuwa yanzu, bisa kokarin da shugabannin kasashen biyu suka yi, dangantakar da ke tsakanin kasahen biyu ta samu bunkasuwa sosai. Shugabannin kasashen biyu sun yi mu'amala da yawa, da ci gaba da kara fahimtar juna a fannin siyasa, kuma an samu sakamako mai kyau wajen yin hadin gwiwa a fannonin tattalin arziki da ba da ilmi da kiwon lafiya, kasashen biyu sun yi hadin gwiwa wajen warware batutuwan kasa da kasa. A ganina, bikin EXPO zai ci gaba da kara fahimtar juna da ke tsakanin jama'ar kasashen biyu, da samar sabuwar damar na bunkasuwar dangantakar da ke tsakaninsu."

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China