in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ranar rumfar Nijer a farfajiyar bikin EXPO na Shanghai
2010-08-03 16:31:32 cri

Cinikayya tsakanin kasashe Sin da Nijer
Tun aka farfado da dangantakar diplomasiyya tsakanin kasashen Sin da Nijer a shekarar 1996, bisa kididdigar da hukumar kwastan ta kasar Nijer ta bayar, an ce, daga shekarar 1996 zuwa ta 2006, adadin kudin da aka samu ta fuskar cinikayyar shige da fice tsakanin kasashen biyu ya kai dala miliyan 246, cinikayyar fitar da kayayyaki zuwa kasar Nijer da Sin ta yi ta samu bunkasuwa yadda ya kamata, abin da ya sa kasar Sin ta daga matsayinta cikin jerin sunayen kasashe wadanda suka fitar da kayayyaki zuwa kasar Nijer daga matsayi na tara a shekarar 1996 zuwa matsayi na uku a shekaru nan bayan da Faransa da Cote Di'voire wadanda suka kasance kasashe masu girma a fannin cinikayya.

Ire-iren kayayyakin da Sin ta fita zuwa Nijer sun karu sosai cikin hada da wasu kayayyaki na zamani da kayayyakin jiyya hakan ya nuna yawan kudin da Sin ta samu wajen fitar da kayayyaki zuwa Nijer ya haura dala miliyan 50 a cikin shekarar 2003, a cikinsu kayayyakin sadarwa sun kwashe kashi 30 bisa 100, ban da wannan kuma, Sin ta ci gaba da kyautata ingancin kayayyaki da take fitar da su zuwa kasashen waje.

A 'yan shekaru da suka gabata, Sin ta shigar da kayayyaki daga kasar Nijer ba da yawa ba, abin da ya sa Sin ta sami rarar kudi da dama. Dalilin da hakan ya haddasa ga wannan shi ne Nijer ta kasa kayayyakin iri-iri wadanda ta fitar da su, ta fitar da ma'adinai Uranium zuwa Faransa da Spaniya da sauran kasashe, kuma ta fitar da amfanin gona zuwa kasashen dake kewayenta da suka hada da Nijeriya da Benin da sauran kasashe, abin da ya sa ba ta iya biyan bukatar kasuwannin kasar Sin ba.

Domin kara taimakawa kasashen Afrika wajen bunkasa tattalin arziki da sa kaimi wajen fitar da kayayyaki zuwa kasar Sin da habaka cinikayya a tsakanin Sin da kasashen Afrika, a cikin shekarar 2004, Sin ta yi alkawarin shigar da kayayyaki daga wasu kasashen Afrika mafi talauci ba tare da buga haraji ba. Ban da wannan kuma, a watan Afrilu na shekarar 2004, Sin da Nijer sun kulla yarjejeniyar samar da gatanci ta fuskar shigar da wasu kayayyaki daga Nijer ba tare da buga haraji ba.

Raya manyan ayyukan more rayuwa a Nijer

Daga shekarar 1974 zuwa shekarar 1992, kasar Sin ta dauki nauyinta domin taimakawa Nijer wajen raya wasu manyan ayyukan more rayuwa da suka hada da yin hadin kai ta fuskar sha'anin noma da madatsar ruwa da diga rijiyoyi da gina filayen wasan motsa jiki da sauransu. Tun kasashen biyu suka farfado da dangantakar diplomasiyya a shekarar 1996, Sin ta taimakawa Nijer wajen gina wasu manyan ayyukan more rayuwa da dama, cikin hada da dakunan jami'ar birnin Niamey da gadar kogin Nijer ta biyu da sauransu. Daga shekarar 2001 zuwa ta 2004, yawan kudin dake shafi ayyukan da Sin ta yi a Nijer ya kai dala miliyan 45.

Yin hadin kai tare da kasar Sin ta fuskar makamashi, in ji firaministan kasar Nijer

A ranar 17 ga watan Satumba na shekarar 2008, wakilin kafar yada labaru ta kasar Sin ya samu hira da firaministan kasar Nijer a wanccan lokaci yayin da halarci bikin rufe gasar wasannin Olympic na birnin Beijing, a lokacin da ya kai masa ziyara domin jinta bakinsa. A tattaunawar sun tabo batutuwan da suka hada da dangantakar cinikayya a tsakanin kasashen biyu a karkashin sabon yanayin tattalin arziki na duniya da tsare-tsaren bunkasa makamashin Nijer da shirin kawar da talauci.(Amina)


1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China