in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ranar rumfar Nijer a farfajiyar bikin EXPO na Shanghai
2010-08-03 16:31:32 cri

Yau ranar 3 ga wata, ana taya murnar ranar rumfar Nijer a farfajiyar bikin EXPO na Shanghai. Mataimakiyar babban sakataren ma'aikatar kasuwanci da masana'antu da matasa 'yan kasuwa ta kasar Nijer Zada Mariama da mataimakin babban wakilin gwamnatin kasar Sin dake bikin EXPO na Shanghai Chen Gonglai sun halarci bikin tare da yin jawabi. Ranar rumfar Nijer rana ce ta cika shekaru 50 da 'yantar da al'ummar kasar Nijer, masu wasan fasaha na kasar Nijer sun yi raye-rayen gargajiya na kabilunsu, gangunan Afrika da raye-raye masu siffar musamman da suka nuna sun burge 'yan kallo sosai.

Mr. Chen gonglai ya nuna yabo ga zumuncin dake tsakanin gwamnatocin kasashen Sin da Nijer da kuma jama'ar kasashen biyu. Ana bikin rumfar kasar Nijer a hadaddiyar rumfar kasashen Afrika, da aka raba ta zuwa yankuna 3 domin nuna biranen kasar da al'adunta da kuma zaman rayuwar jama'arta. Mataimakiyar babban sakataren ma'aikatar kasuwanci da masana'antu da matasa 'yan kasuwa ta kasar Nijer Zada Mariama wadda ke halartar bikin ta bayyana cewa, bikin EXPO na Shanghai zai bunkasa huldar hadin gwiwa ta sada zumunci dake tsakanin kasashen Sin da Nijer.(Lami)

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China