in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ranar rumfar Nijer a farfajiyar bikin EXPO na Shanghai
2010-08-03 16:31:32 cri

Rumfar Nijer a farfajiyar bikin EXPO na Shanghai

A dakin dake nuna yadda birane ke kasancewa a kasar Nijer, za ka ga halin da birane ke ciki a kasar, da irin albarkatun da ake samu a birane, da yadda zaman rayuwar mazaunan birane ya ke, da bayyanawa yadda ake kokarin bunkasa biranen kasar.
A dakin al'adu, an kafa wani kayan tsafi mai launin shudi a jikin bango mai fari, wannan ya bayyana irin gidaje na musamman a kasar Nijer. Kana an nuna kayayyakin tarihi da ke bayyana al'adun kasar mai shekaru dubu 6.
A dakin dake bayyana yadda zaman rayuwar jama'a ke kasancewa, an bayyana halin da aikin noma da kiwon dabbobi a kasar Nijer suke, kana an gabatar da batun yin amfani da albarkatun birane da al'adun kabilu da kuma raya birane bisa daidaici. Hotuna da kayayyaki da kuma wasannin gargajiya za su sa masu kallo su kara fahimtar halin zaman rayuwa da mutanen kasar Nijer suke ciki.

Bunkasuwar dangantakar siyasa dake tsakanin Sin da Nijer

A shekarar 1960, firaministan kasar Sin na lokacin Zhou Enlai ya taba taya kasar Nijer murnar samun 'yancin kai, da amincewa da ita.

Bayan da aka kafa gwamnatin soja a kasar Nijer a karkashin shugabancin Seyni Kountche, an tura tawagar sada zumunta da mataimakin shugaban kwamitin soja ya shugabanta zuwa kasar Sin a watan Yuli na shekarar 1974, kana ta daddale sanarwar kulla dangantakar diplomasiyya tsakanin Nijer da Sin da yarjejeniyar hadin gwiwar fasahohin tattalin arziki a ran 20 ga watan Yuli na wannan shekara. Daga baya, an inganta dangantakar hadin gwiwar sada zumunta a tsakaninsu, da kara yin mu'amala da juna. Shugaba Kountche ya kai ziyara a kasar Sin har sau biyu, wato a shekarar 1977 da ta 1984, kuma sauran shugabannin kasar su ma sun kawo ziyara a kasar Sin. A shekarar 1978, mataimakin shugaban majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Ji Pengfei da ministan ciniki Liu Yi da sauran shugabannin kasar Sin sun kai ziyara a kasar Nijer.

Yayin da Ali Saibou ya hau kujerar shugabancin kasar Nijer, an ci gaba da inganta dangantakar abokantaka a tsakanin kasashen biyu. A shekarar 1990, ministan kula da harkokin hadin gwiwa da diplomasiyya na kasar Nijer ya shugabanci wata tawaga da ta kawo ziyara a kasar Sin, kuma ministan kula da harkokin ma'adinai na kasar Sin Zhu Xun da sauran ministocin kasar sun kai ziyara a kasar Nijer. Amma a karshen wa'adin lokacin gwamnatin wucin gadi ta kasar Nijer, wasu 'yan siyasa na kasar Nijer sun amince da manufar diplomasiya da yankin Taiwan ya ayyana, da kulla huldar diplomasiyya a tsakanin kasarsu da yankin Taiwan a ran 22 ga watan Yuli na shekarar 1992. Sabo da haka, kasar Sin ta sanar da yanke huldar diplomasiyya a tsakaninta da kasar Nijer a ran 30 ga watan Yuni a wannan shekara.

Bayan da aka kafa jamhuriyya ta 4 a Nijer, shugaban kasar Ibrahim Bare Mainassara ya tsaida kudurin sake kulla huldar diplomasiyya a tsakanin kasarsa da kasar Sin. A ran 19 ga watan Agusta na shekarar 1996, kasashen biyu sun sa hannu kan hadaddiyar anarwar sake kulla huldar diplomasiyya. Bayan haka, an mayar da dangantakar hadin gwiwa a tsakaninsu. A watan Janairu na shekarar 1997, mataimakin firaministan kasar Sin kuma ministan harkokin waje na kasar Qian Qichen ya kai ziyara a kasar Nijer, kana a watan Mayu a wannan shekara, shugaban kasar Nijer Bare ya kawo ziyara a kasar Sin. Shugabannin kasar Nijer sun tsaya tsayin daka kan manufar Sin daya tak, da amincewa da yankin Taiwan wannan wani muhimmin batu ne ga kasar Sin, da nuna goyon baya ga kasar Sin da ta kammala aikin samun dinkuwar kasar baki daya, da mai da kasar Sin a matsayin abokiyar kasashe masu tasowa da muhimmiyar abokiyar hadin gwiwa ta kasar Nijer.

Bayan da Daouda Malam Wanke ya yi juyin mulki a kasar Nijer a shekarar 1999, kasar Sin ta yi la'akari da huldar dake tsakanin kasashen biyu, da bayyana ra'ayinta na rashin tsoma baki a cikin harkokin kasashen waje, da gayyatar ministan harkokin waje na gwamnatin wucin gadi ta kasar Nijer da ya kai ziyara a kasar Sin, da kuma ci gaba da gudanar da ayyukan hadin gwiwa da kasashen biyu suka tsara. Gwamnatin wucin gadi ta kasar Nijer ta nuna godiya ga kasar Sin, da jaddada tsayawa tsayin daka kan manufar Sin daya tak da sada zumunta a tsakaninta da kasar Sin.

Bayan da aka kafa jamhuriyya ta 5 a Nijer, shugaban kasar Mamadou Tandja ya ci gaba da sada zumunta a tsakanin kasarsa da kasar Sin, da nuna yabo ga hanyar da kasar Sin ta bi wajen samun bunkasuwa, da darajanta hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu, kuma an inganta dangantakar dake tsakaninsu. Ban da wannan, gwamnatoci da majalisun dokokin kasashen biyu sun kiyaye yin mu'amala da juna. A watan Yuni na shekarar 2001, shugaban kasar Nijer Tandja ya kai ziyara a kasar Sin, kana a watan Agusta na shekarar 2003, firaministan kasar Hama Amadou shi ma ya kawo ziyara a kasar Sin, sabo da haka, an inganta dangantakar abokantaka a tsakaninsu. A gun taron kwamitin kare hakkin bil Adam na MDD a karo na 56 da na karo na 57, kasar Nijer ta nuna goyon baya ga shirin da kasar Sin ta gabatar, da ba da taimako ga kasar Sin wajen yaki da shirin nuna adawa ga kasar Sin da kasar Amurka ta bayar.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China