in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hadaddiyar rumfar kasashen Afrika ta zama babban dandalin nuna al'adunsu
2010-07-16 16:02:07 cri

Babban wakilin rumfar kasar Cape Verde Joao Vieira shi ma ya nuna yabo ga taimakon da kasar Sin ta bai wa kasashe masu tasowa da suka shiga bikin EXPO. Ya ce, "Abin da ya kamata in ambata shi ne, a yayin bikin EXPO na wannan karo, kasar Sin ta bai wa kasashe masu tasowa taimako da yawa. Ba don irin wannan taimako ba, ba za mu shiga bikin EXPO yadda ya kamata ba."

A cikin hadaddiyar rumfar kasashen Afrika, kasuwar Afrika ta jawo hankalin mutane sosai. Wani 'dan kasuwa mai sayar da kayayyakin da aka saka da hannu mai suna Zeca Logomale ya ce, a cikin rumfar, masu yawon shakatawa suna iya gannin kayayyakin da aka saka da hannu iri daban daban na Afrika. Ya kuma kara da cewa, "Shekaru na biyu ban koma gida ba, amma a yayin da na shiga wannan rumfar, na ji kamar ina garina dake Afrika. Hadaddiyar rumfar kasashen Afrika wata kyakkyawar rumfa ce."(Lami)


1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China