in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hadaddiyar rumfar kasashen Afrika ta zama babban dandalin nuna al'adunsu
2010-07-16 16:02:07 cri

Jama'a masu sauraro, wakar da kuka saurara waka ce da kungiyar kide-kide ta Alves Brader's ta rera. 'Yan uwa guda 3 ne suka kafa wannan kungiyar kide-kide, wadda ta shahara sosai a kasar Cape Verde. Shugaban kungiyar To Alves ya ce, "Na yi murna da bikin EXPO na Shanghai sabo da ya samar mana damar musayar ra'ayi da mutanen sauran kasashen duniya da kuma sanin al'adunsu, ina fatan za a cimma nasarar bikin EXPO na Shanghai."

Domin taimakawa kasashen Afrika wajen nuna al'adunsu da kyau, gwamnatin kasar Sin ta taimaka musu a fannin gina rumfuna da inganta tattalin arziki. A game da haka, jami'an gwamnatoci da jami'an rumfunan wasu kasashen Afrika sun nuna godiya ga kasar Sin. Ministar ciniki da masana'antu ta kasar Ghana Hanna Tetteh ta nuna godiya a gun bikin murnar ranar rumfar kasar Ghana tana cewa, "A madadin shugaban kasar Ghana da kuma jama'ar kasar, ina son nuna godiya ga gwamnatin kasar Sin da kuma jama'arta, sabo da shirya bikin EXPO na Shanghai, kana suka gayyace mu. A sa'i daya, na nuna godiya ga kasar Sin sabo da taimakon da ta bai wa kasar Ghana, sabo da haka, kasar Ghana ta iya shiga bikin EXPO yadda ya kamata."

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China