A ran 1 ga watan Nuwamba na shekarar 2007, a yayin da kasar Libya ta yanke shawarar shiga bikin EXPO na Shanghai, kasashe 48 na Afrika da suka kulla huldar diplomasiyya tare da kasar Sin dukkan su sun tabbatar da shiga bikin EXPO na Shanghai. Hadaddiyar rumfar kasashen Afrika dake sashe na C ta farfajiyar bikin ta hada da rumfunan kasashe 43 na Afrika da kuma rumfar kungiyar tarayyar kasashen Afrika. A wannan rumfar, an baje kolin tufafi da abinci da kide-kide da raye-raye, masu yawon shakatawa suna iya ganin ire-iren al'adun da Allah ya horewa kasashen Afrika su da kansu.